Ina sane da kalubalan Najeriya - Buhari

Ina sane da kalubalan Najeriya - Buhari

- Shugaba Muhammadu Buhari yace yana sane da kalubalen da Najeriya ke fuskanta

- Ya kara jadadda jajircewar gwamnatinsa wajen magance matsalolinm

- Shugaban kasar ya roki al’umman kasashen waje da su goyi bayan jajircewar Najeriya don rage illar canjin yanayi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace fitar Najeriya daga cikin mawuyacin tattalin arziki, bai kasance mafarki ba kan yawancin matsaloli da kasar ke fuskanta.

NAIJ.com ta tattaro cewa mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya fada a wani jawabi da ya gabatar a ranar Talata, 13 ga watan Disamba, cewa shugaban ya bayyana tawali’un ne a taron One Planet Summit a kasar Faransa.

Ina sane da kalubalan Najeriya - Buhari

Ina sane da kalubalan Najeriya - Buhari

"Bayan fita daga koma bayan tattalinarziki, bamu kasance masu mafarki ba kan kalubale da muke fuskanta a Najeriya,”a cewar shugaban kasar.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kashe wani tsohon kwamishinan Bayelsa

Buhari har ila yau ya roki al’umman kasashen waje da su goyi bayan jajircewar Najeriya don rage illar canjin yanayi.

Ya fada wa shuwagabanni fiye da 60 da suka halarci taron, har da wakilai masu wakiltan hukumomi masu zaman kansu da suka halarci taron mai taken“Climate Change Financing,” cewa kasar bazata iya aiwatar da taimako da ta kayyade wa al’umma ba sai dai da goyon bayan kasashe masu matukar cigaba ta hanyar samar da isashen kudade, fasaha da gina masu aiki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200

Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200

Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200
NAIJ.com
Mailfire view pixel