Turai na da hannu a cin zarafin 'yan ci-rani a Libya – Kungiyar kare hakkin dan Adam

Turai na da hannu a cin zarafin 'yan ci-rani a Libya – Kungiyar kare hakkin dan Adam

Kungiyar nan dake kare hakkin dan Adam wato Amnesty International ta zargi gwamnatocin kasashen Turai da hannu dumu-dumu wajen cin zarafin bakaken fata dake gudun hijira a kassar Libya.

Zargin kungiyar na kunshe ne a wani rahoto da ta fitar inda ta kara da cewa a kokarinta na dakile kwararar bakin haure, kungiyar tarayyar Turai tana taimaka wa "wani shirin cin zarafin" bakaken fata a gabar tekun Libiya.

Kudaden kungiyar tarayyar Turai suna zuwa ga hukumomin dake aiki da mayaka da kuma masu safarar mutane, a cewar rahoton.

Turai na da hannu a cin zarafin 'yan ci-rani a Libya – Kungiyar kare hakkin dan Adam
Turai na da hannu a cin zarafin 'yan ci-rani a Libya – Kungiyar kare hakkin dan Adam

Kungiyar tarayyar Turai ta bayar da jiragen ruwa da horaswa da kuma kudi ga jami'an tsaron gabar tekun Libiya.

KU KARANTA KUMA: Ba kamar zamaninmu ba, matasan yanzu na goyon bayan cin hanci da rashawa - Amaechi

Kasar Libya ita ce hanyar da 'yan ci-rani masu son zuwa Turai suka fi bi wurin isa Italiya.

Amma Amnesty ta ce jam'ian tsaron suna aiki da 'yan daba masu laifi da kuma masu safarar mutane wadanda aka samu da laifin nau'o'i na cin zarafi, da sanin jami'an kungiyar tarayyar Turai.

Kungiyar Amnesty ta yi zargin cewa kokarin dakile kwarar bakin haure ya janyo "kama mutane da yawa da kuma daure su ba gaira ba dalili".

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel