Amnesty International ta bukaci a yi wa 'yan Shi'a da aka kashe adalci

Amnesty International ta bukaci a yi wa 'yan Shi'a da aka kashe adalci

- Amnesty International ta nace akan adalci ga ‘yan Shi’a wadanda sojoji suka kashe a Zaria

- Kungiyar ta ce dole ne gwamnatin Najeriya ta caje sojojin da suka aikata laifin kisan

- Amnesty ta bukaci ministan shari'a ya umarci tono gawawwakin daga inda aka binne su

Kungiyar Amnesty International ta jaddada matsayin ta cewa dole ne gwamnatin Najeriya ta tabbatar da adalci, gaskiya da kuma caje sojojin da suka yi wa 'yan Shi'a fiye da 350 kisan gilla a birnin Zaria a watan Disamba na shekarar 2015.

Kungiyar ta bayyana hakan ne yayin bikin ranar tunawa na shekara 2 da aka yi wa daruruwan ‘yan Shi’a kisan gilla.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, darakta na Amnesty International a Najeriya, Osai Ojigho, ya ce babu wanda gwamnati harzu ta zargi da alhakin wannan kashe-kashen, yayin da iyalan wadanda ake zato ba san inda suke ba suna jiran labarai na 'yan uwa. Amnesty International ta ce ta gano da kuma ziyarci wani wurin da take zargi an binne ‘yan Shi’a a kusa da Mando, amma har yanzu ba a tona gawawwakin daga kaburbura ba.

Amnesty International ta nace akan adalci shekaru 2 bayan kisan daruruwan ‘yan Shi’a
'Yan kungiyar Shi'a

“Yawancin iyalai har yanzu ba su san halin da 'yan uwansu suke ciki ba, waɗanda ba a gani ba tun faruwar rikicin tun Disamba 12, 2015”, in ji Osai Ojigho.

KU KARANTA: Mulki kama karya na sojoji ya haifar da rudnunar yansandar SARS – Femi Falana

"Babban mai shari'a kuma ministan shari'a na tarayya ya umarci tono gawawwakin, kuma wadanda ake zargi da alhakin kisan gilla su fuskanci shari'a".

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel