Da kudin sata aka yi wa Buhari yakin neman zabe Inji wata ‘Yar Majalisa

Da kudin sata aka yi wa Buhari yakin neman zabe Inji wata ‘Yar Majalisa

- Wata ‘Yar Majalisa tayi kaca-kaca da Shugaban Kasa Buhari

- Honarabul Binta Bello tace da kudin sata Buhari ya dare mulki

- ‘Yar Majalisar tace babu dalilin da zai sa Shugaban ya soki PDP

Wata ‘Yar Majalisar Tarayyar Najeriya Honarabul Binta Bello ta yi kaca-kaca da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari inda tace karewar ta ma da kudin sata Buhari ya samu ya dare mulki.

Da kudin sata aka yi wa Buhari yakin neman zabe Inji wata ‘Yar Majalisa

‘Yar Majalisa tayi kaca - kaca da Gwamnatin Buhari

Wannan babbar ‘Yar Majalisar Wakilan Kasar tace barayin PDP ne su ka yi wa Shugaban Kasar yakin neman zabe a 2015 don haka babu dalilin da zai sa ya fito ya rika sukar Jam’iyyar adawar sai dai ma ya ba ‘Yan Najeriya hakuri saboda gazawar sa.

KU KARANTA: Shugaban Kasa Buhari ya isa Kasar Faransa domin wani taro

Binta Bello ta fadawa Jaridar Punch cewa Shugaba Buhari ya gaza cika duk alkawarun da ya dauka kafin a zabe sa. ‘Yar Majalisar ta kalubalanci Shugaban Kasar ya bayyanawa mutanen Najeriya kasafin kudin bana da kuma aikin da aka yi a Kasar.

Honarabul Bello dai tace har yanzu Jam’iyyar PDP da tayi mulki tana da abin nunawa ba kamar Gwamnatin Buhari ba. ‘Yar Majalisar tace kafin 2015 Shugaban Kasar bai da dukiyar da zai lashe zabe don haka wadanda yake kira barayi su ka dafa masa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hotunan Osinbajo yayin da yake turance larabawa a wurin taron kasa da kasa a Dubai

Hotunan Osinbajo yayin da yake turance larabawa a wurin taron kasa da kasa a Dubai

Osinbajo ya turance larabawa a taron kasa da kasa a Dubai, kalli hotuna
NAIJ.com
Mailfire view pixel