An karrama shugabannin Izala da takardar girmamawa a kasar Spain

An karrama shugabannin Izala da takardar girmamawa a kasar Spain

- Wani kungiyar addinin musulunci a kasar Spain ta karrama shugabannin Izala biyu da takardar girmamawa

- Kungiyar ta ce ta girmamawa malaman bayan gagarumar nasarorin da suka samu na da'awa da yada Sunnah a kasashen turai

Wani kungiyar addinin musulunci a kasar Spain wato kungiyar Wa'azin Musulunci ta Sautus Sunnah Europe mai rassa a kasashen Turai, ta karrama shugaban kungiyar jamaatu Izalatil bidah wa ikamatissunnah biyu Sheikh Abdullah Bala Lau da babban sakataren kungiyar, Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe da shaidar shaida na girmamawa.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari , kungiyar ta bayyana cewa wannan lambar yabo ta biyo bayan gagarumar nasarorin da suka samu na da'awa da yada Sunnah wanda suka dauki kusan makwanni biyu suna yi a kasashen turai.

Kungiyar Musuluncin ta karrama Maluman ne a babban Masallacin Juma'a na Masjidul Huda da ke birnin Barcelona a kasar Spain bayan kammala Muhadharah wacce manyan Maluman suka gabatar.

An karrama shugabannin Izala da takardar girmamawa a kasar Spain
Yayin karrama shugabannin Izala da takardar girmamawa a kasar Spain

KU KARANTA: 2019: Musulmai su guji zagin juna a kan harkar siyasa Inji Gumi

Masoya malaman daga cikin masallacin suna ta kabbara yayin da ake gabatar musu da takardar girmamawa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel