Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf

Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf

Kungiyar nan wadda ba ta gwamnati ba dake rajin kare muradun al'umma da suka jibanci tattalin arziki da 'yanci watau Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP) ta yabawa shugaban kasa game da rantsar da kwamitin binciken kudade da kadarorin satar da aka kwato.

Haka nan kuma dai sai kungiyar ta Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP) ta bukaci shugaban da ya kara karfin gilashin kwamitin binciken ya zuwa sauran gwamnatocin da shuka shude a bayan sa domin samun cikakken rahoto.

Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf

Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf

KU KARANTA: Kashi 70 na daliban Arewa jahilai ne - Masani

NAIJ.com dai ta samu cewa wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar Asabar, 9 ga watan Disembar shekarar 2017 dauke da sa hannun shuganan ta Adetokunbo Mumuni inda ya shawarci shugaba Buhari din da ya kuma kara tsawon wa'adin kwamitin daga sati hudu zuwa wata shidda.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a cikin watan da ya gabata ne shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani kwamiti na mutum uku da zai yi bincike game da kudade da kadarorin satar da aka kwato.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain NAIJ.com HAUSA

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200

Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200

Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200
NAIJ.com
Mailfire view pixel