Wani ya kashe Mahaifiyar sa a wata Kasa bayan sun samu ‘dan rikici

Wani ya kashe Mahaifiyar sa a wata Kasa bayan sun samu ‘dan rikici

- Kwananaki wani Saurayi ya aika mahaifiyar sa lahira

- Yanzu haka Jami’an ‘Yan Sandan Kasar sun yi ram da shi

- Wannan saurayi ya datsewa uwar sa kai ya dauki bidiyo

A makon jiya mu ka ji labari cewa wani yaro ya kashe Mahaifiyar sa a Kasar Sin bayan sun samu rikicin da bai kai ya kawo ba a kwanaki kamar yadda Gidan BBC Hausa ta kawo rahoto. Sai daga baya ne aka san cewa an yi wannan kisar gilla.

Wani ya kashe Mahaifiyar sa a wata Kasa bayan sun samu ‘dan rikici
Yaro ya aika Mahaifiyar sa lahira a Kasar China

Ana zargin annan yaro ya kashe Mahaifiyar sa, ya kuma datse mata kai. Bayan yaron ya kashe Mahaifiyar ta sa, ya dauki bidiyo ya yada a shafin sa na WeChat. Wannan abu ya faru ne a Garin Wenxing da ke yankin Sichuan na Kasar Sin.

KU KARANTA: An kama wadanda ake zargi da laifin sace wani Shugaban Matasa a Kaduna

Maganar ta fashe ne kwanaki bayan abin ya faru inda abokin wannan yaro ya nunawa Mahaifiyar sa wannan bidiyo. Jami’an ‘Yan Sanda dai sun yi bincike inda mu ka samu labari cewa kawo yanzu an kama wannan yaro da ake zargi da laifin kisa.

Kamar yadda rahoton Gidan BBC Hausa ya nuna, ‘Yan Sanda sun tabbatar da cewa an kama wannan yaro amma har yanzu ba ayi wani karin bayani ba. Yaron dai ya kashe mahaifiyarsa ne bayan da suka yi sa'insa a ranar Lahadi da daddare.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel