Abun babba ne: Isra'ila ta fara ruwan bama-bamai a Zirin Gaza

Abun babba ne: Isra'ila ta fara ruwan bama-bamai a Zirin Gaza

Rahotanni daga kasar Isra’ila na nuna cewa rundunar sojin kasar sun bayyana cewaq, jiragen sama da tankokin yakin ta sunyi rowan bama-bamai a Zirin Gaza da Yahudawa suka mamaye.

Sanarwar ta yi Karin haske da cewa, wasu jiragensu tare da tankokin yaki ne suka kai harin a Gaza inda suka nufi kungiyoyin yan ta'adda.

Sanarwar ta kuma ce, an kai harin ne domin mayar da martani ga wasu makaman roka 3 da aka harba zuwa Kudancin Isra'ila daga Zirin na Gaza.

Abun babba ne: Isra'ila ta fara ruwan bama-bamai a Zirin Gaza
Abun babba ne: Isra'ila ta fara ruwan bama-bamai a Zirin Gaza

An bayyana cewa, 2 daga cikin makaman na Roka sun afka wani waje da babu komai a Kudancin Isra'ila kuma ba su janyo wata barna ba.

KU KARANTA KUMA: Manyan nasarori da hukumar Kwastam tayi wajen kwace haramtattun kayayyaki a kasar (hotuna)

Babu wata kungiyar Falasdinawa da ta dauki alhakin kai harin makamin na roka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel