Dandalin Kannywood: Muhimmiyar wasiyyata ga masu son koyi da ni a duniya - Nafisa Abdullahi

Dandalin Kannywood: Muhimmiyar wasiyyata ga masu son koyi da ni a duniya - Nafisa Abdullahi

Gogaggiyar jarumar nan ta wasannin fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood ta yi nasiha ga masoyan ta mata musamman ma masu so su yi koyi da ita a ruwar duniya ganin yadda ta samu nasarori da dama a harkar fim tare da lashe kambun kyaututtuka da dama.

Jarumar dai tayi wannan nasihar ne ga dumbin masoyan nata ne yayin da take fira da majiyar mu jim kadan bayan ta amshi kyaura jarumar-jarumai a fina-finan kasashen Afrika a wajen wani bikin karramawa da aka yi a birnin Landan a cikin watan da ya gabata.

Dandalin Kannywood: Muhimmiyar wasiyyata ga masu son koyi da ni a duniya - Nafisa Abdullahi
Dandalin Kannywood: Muhimmiyar wasiyyata ga masu son koyi da ni a duniya - Nafisa Abdullahi

KU KARANTA: Hanyoyi 5 da zaku kula da jikin ku cikin sanyi da baku sani ba

Legit.ng dai ta samu cewa da aka tambaye ta ko meye shawarar ta ga mata musamman ma masu sha'awar sana'ar fim din da kuma suke kallon ta a matsayin wata abar koyi a duniya, sai ta kada baki tace tana shawartar su da su kasance kan su kawai ba tare da kwaikwayon kalar rayuwar wasu ba.

A cewar ta, dukkan wadda ta ke so ta zama tauraruwa to dole ne ta guji kwaikwayon rayuwar wasu, ya kamata su zama masu yin irin rayuwar su ta kansu ba ta kwaikwayo ba ko karya sannan kuma su dage da yin aiki tukuru.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Online view pixel