Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya dawo gida Najeriya (hotuna, bidiyo)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya dawo gida Najeriya (hotuna, bidiyo)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo gida Najeriya daga kasar Jordan bayan ya halarci taron magance ta’addanci.

Hakan na kunshe ne a cikin rubutu da Bahir Ahmad, hadimin shugaban kasar ya wallafa a shafinsa na twitter a ranar Litinin, 4 ga waran Disamba.

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya dawo gida Najeriya (hotun, bidiyo)
Shugaba Buhari ya dawo gida Najeriya

A baya Legit.ng ta rahoto cewa shugaban kasar ya bar gida Najeriya zuwa kasar Jordan a ranar Juma’a, 1 ga watan Disamba.

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya dawo gida Najeriya (hotun, bidiyo)
Shugaba Buhari na gaisawa da ministan harkokin waje bayan dawowarsa daga Jordan

KU KARANTA KUMA: Barin APC shine babban kuskure da Kwankwaso zai yi a rayuwarsa – Tsohon hadimin sa

Shugaba Buhari ya hadu da sarkin Jordan, Abdullahi II wanda ya fada masa cewa akwai bukatar hadin gwiwar yankuna domin magance barazanar duniya ta fannin ta’addanci.

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya dawo gida Najeriya (hotun, bidiyo)
Shugaba Buhari na gaisawa da gwamnoni bayan dawowarsa daga Jordan

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=e

Asali: Legit.ng

Online view pixel