Hukuncin dauri na shekara 3 zai tabbata kan duk wanda ya yiwa matar sa saki 3 lokaci guda a kasar India

Hukuncin dauri na shekara 3 zai tabbata kan duk wanda ya yiwa matar sa saki 3 lokaci guda a kasar India

Kasar India tayi shirin daukar hukunci akan duk wani namiji da ya yiwa matar sa saki uku a lokaci guda, inda zai fuskanci hukunci dauri na zama a gida kaso har na tsawon shekaru uku.

Rahotanni sun bayyana cewa, gwamnatin kasar ba za ta tsaya a haramta saki ukun kadai ba, domin kuwa har dauri na tsawon shekaru uku mazajen zasu fuskanta, domin su dauki rikon igiyar aure da muhimmanci.

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan doka zata takaita ne kadai akan musulmai wanda sune mafi karanci a kasar.

Wannan yunkuri na gwamnatin kasar India zai baiwa mata dama ta samun wurin zama a gidajen mazajen su tare da ceton yara da rayuwar su ke gurbacewa sakamakon rabuwar aure a tsakanin iyayen su.

Yayin gudanar da bikin aure a kasar India
Yayin gudanar da bikin aure a kasar India

Dokar ta zo ne da sanadin jagorancin ministan cikin gida na kasar; Rajnath Singh, inda sauran 'yan kwamitin suka hadar da Ministan harkokin kasashen ketare; Sushma Swaraj, Ministan Kudi; Arun Jaitley da kuma ministan shari'a Ravi Shankar Prasad.

KARANTA KUMA: Tashin-tashina yayin da kungiyar Shi'a tayi arangama da jami'an 'yan sanda a jihar Kaduna

Sai dai wasu da dama suna ikirarin babu ambaton wannan doka a Al-Qur'ani ko Hadisi, domin kuwa musulunci ya baiwa miji dama ta yiwa matar sa saki uku a lokaci guda da ya furta da baki.

Wannan doka ba bakon abu bace a kasashen musulmai irin su Pakistan da Bangladesh, sai dai abin yazo ne a kasar ta India sakamakon mace-macen aure wanda hukumomin kasar suke ganin ya kamata a dauki mataki.

A yadda wani mazaunin kasar Heena Khan, wanda yake bincike akan matsalolin aure ya bayyana cewa, "cikin shekarun da suka gabata, fiye da mata dubu musamman wadanda suka fito daga gidajen da ake fama da halin rayuwa, mazajen su sukan yi watsi da su wanda hakan yake janyo koma baya a cikin kasar."

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel