Bayan shan suka shugaban mabiya addinin Kirista na duniya ya ambaci Musulman Rohingya

Bayan shan suka shugaban mabiya addinin Kirista na duniya ya ambaci Musulman Rohingya

- Fafaroma Francis ya ambaci Musulman Rohingya a jawabin sa ga dimbin 'yan gudun hijira a kasar Bangladesh

- Masu suka sun yi ca a kan Fafaroma Francis bayan ya ki ambaton musulmin Rohingya ko nuna alhinin halin da suke ciki a wata ziyarar kwanaki hudu da ya kai kasar Myanmar watan da ya gabata

- A baya Fafaroma Francis ya samu yabo a matsayin mai nemawa 'yan gudun hijira da kananun kabilu 'yanci ba tare da la'akari da addinin su ba

Bayan shan suka shugaban mabiya addinin Kirista na duniya ya ambaci Musulman Rohingya
Musulman Rohingya

Saidai ya sha suka lokacin da ya yi wata ganawa da shugabar kasar Myanmar, Aung Sang Suu, amma yaki ambaton musulmi 'yan kabilar Rohingya dake fuskantar kisan kare dangi a hannun mabiya addinin Kirista na kasar.

DUBA WANNAN: Gasar kofin kwallon kafa ta duniya: Najeriya zata kara da kasashen Argentina, Crotia, da Iceland, a rukunin D

Fiye da mutum 600,000 'yan kabilar Rohingya na zaune a kasar Bangladesh a matsayin 'yan gudun hijira.

'Yan kabilar Rohingya na fuskantar nuna wariya daga hukumomi a kasar Myanmar.

'Yan jarida da kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun kwarmata halin cin mutuncin 'yan kabilar Rohingya da sojoji a kasar Myanmar ke cigaba da aikatawa amma har yanzu shugabar kasar Aung San Suu taki amincewa da hakan na faruwa balle har ta dauki mataki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel