Hamshaƙin attajirin Najeriya, Dangote, ya gina katafaren kamfanin Siminti a ƙasar Congo

Hamshaƙin attajirin Najeriya, Dangote, ya gina katafaren kamfanin Siminti a ƙasar Congo

Shahararren attajirin nan dan Najeriya, Aliko Dangote ya kaddamar da katafaren kamfanin Siminti na rukunin kamfanuwan Dangote a kasar Congo dake yankin gabashin Afirka.

Kamfanin dillancin labaru ta ruwaito Attajirin ya gina kamfanin ne da dalan miliyan 500, wanda ake sa ran zata dinga fitar da tan miliyan 1 da 500,000 na Siminti a duk shekara.

KU KARANTA: Sojoji sun ceto mutane 212 tare da kama kwamandan Boko Haram

Hamshaƙin attajirin Najeriya, Dangote, ya gina katafaren kamfanin Siminti a ƙasar Congo
Kamfani

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kamfanin zata samar da ayyuka 1000 kai tsaye, da daruruwan ayyukan a kaikaice. Da bikin kaddamar da wannan kamfani, Dangote na da kamfanuwan Siminti guda goma kenan a nahiyar Afirka.

Hamshaƙin attajirin Najeriya, Dangote, ya gina katafaren kamfanin Siminti a ƙasar Congo
Kamfanin

Shi kan sa shugaban kasar Congo, Denis Sassou Nguesso na daga cikin wandanda suka halarci taron, inda har ya mika masa lambar girmamawa ta kasar Congo. Haka zalika Firai ministan kasar Clement Moumba.

Hamshaƙin attajirin Najeriya, Dangote, ya gina katafaren kamfanin Siminti a ƙasar Congo
Shugaban Congo da Dangote

Daga Najeriya taron ya samu halartar ministan ma’adanai, Kayode Fayemi, ministan ciniki, Okechukwu Enelamah, shugaban kamfanin BUA, Abdulsamad Rabiu, tsohon babban Sufetan Yansanda, Abubakar Mohammed, Adams Oshiomale da sauran jiga jigan kamfanin Dangote.

Hamshaƙin attajirin Najeriya, Dangote, ya gina katafaren kamfanin Siminti a ƙasar Congo
Manyan baki

Hamshaƙin attajirin Najeriya, Dangote, ya gina katafaren kamfanin Siminti a ƙasar Congo
Kamfanin

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel