Kungiyar Izala ba ta karbi kudin Makamai ba – Kabiru Gombe

Kungiyar Izala ba ta karbi kudin Makamai ba – Kabiru Gombe

Rahotanni sun kawo cewa Sheikh Kabiru Gombe, daya daga cikin yan kungiyar Izala, ya yi watsi da jita-jitan cewa kungiyar su ta Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah ta karbi wani kaso daga kudin makamai.

Kabiru Gombe ya sanar da hakan ne a wata ziyara da ya kai ofishin BBC Hausa a birnin Landan tare da rakiyar shugaban kungiyar Sheikh Abdullahi Bala Lau.

A hirar da ya yi da BBC Hausa, Kabiru ya ce babu shakka kungiyar Izala ta bukaci taimako daga gurare da dama domin gudanar da wasu ayyukan ta da ya hada da bude gidan talabijin na Manara TV, amma kungiyar ba ta da alaka ta kusa ko ta nesa da maganar karbar kudin makamai.

Kungiyar Izala ba ta karbi kudin Makamai ba – Kabiru Gombe
Kungiyar Izala ba ta karbi kudin Makamai ba – Kabiru Gombe

Ya kara da cewa duk inda suka sami gudunmawa sai da suka tabbatar hanya ce da ta dace.

KU KARANTA KUMA: Osinbajo ya kaddamar da fasa kauri a matsayin barazana ga tattalin arzikin Najeriya

“Ba mu da alaka ta kusa ko ta nesa da maganar karbar kudin makamai. Wannan abu ne da kungiyar Izala ba ta taba shiga cikin shi ba.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel