Sanata Shehu Sani yayi kaca-kaca da 'yan a-mutun Shugaba Buhari

Sanata Shehu Sani yayi kaca-kaca da 'yan a-mutun Shugaba Buhari

Fitaccen Sanatan nan kuma mamba a majalisar dattijan Najeriya dake wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani yayi kaca-kaca da masu kiran kan su 'yan amutun shugaba Buhari, inda ya bayyana su a matsayin mayaudara masu son kare muradun kansu-da-kansu kawai.

Sanatan yayi wannan ikirarin ne a shafin sa na Tuwita a jiya inda yake shagube ga da yawa daga cikin na su a cikin wani irin salo na zolaya da kuma hannun-ka-mai-sanda.

Sanata Shehu Sani yayi kaca-kaca da 'yan a-mutun Shugaba Buhari

Sanata Shehu Sani yayi kaca-kaca da 'yan a-mutun Shugaba Buhari

KU KARANTA: An tsimci gawar wani jigo a jam'iyyar APC a Katsina

NAIJ.com dai ta samu cewa Sanatan dai ya kuma bayyana cewa da yawa daga cikin masu kiran kansu da wannan sunan a yanzu ba su kira kansu da hakan ba a lokacin da shugaban bai zama kowa ba sannan kuma tabbas da zaran ya sauka za su sake gudun sa.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a cikin satin da ya gabata ma dai mun ruwaito maku cewa Sanata Shehu Sani ya bayyana cikakken goyon bayan sa ga daya daga cikin jikon jam'iyyar ta APC Cif Bola Tinubu game rashin dacewar ba Shugaba Muhammadu Buhari tikitin takara a 2019 kai tsaye.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain NAIJ.com HAUSA

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Labari na musamman: Yadda wani ‘dan acaba ya kashe ‘Dalibar A.B.U

Labari na musamman: Yadda wani ‘dan acaba ya kashe ‘Dalibar A.B.U

Cikakken labari: Yadda wani ‘Dan acaba ya kashe ‘Dalibar A.B.U Zaria
NAIJ.com
Mailfire view pixel