Wata mata ta shafe wata 9 tana haukan karya domin kare 'yar ta daga Boko Haram

Wata mata ta shafe wata 9 tana haukan karya domin kare 'yar ta daga Boko Haram

- Wannan al'amari ya faru ne a garin Madagali na Jihar Adamawa

- Matar ta boye 'yar tata a rami mai zurfi sai kuma ta fake da haukan karya

- Matar ta rika wasa da kasa da har ma ta shafe jikinta da fitsari da bayan gida domin ta gamsar dasu hauka take

Sakamakon wulakanci da tozarci da 'yammata su ke fuskanta a hannun 'yan boko haram, wata mata mai suna Hamayaji, ta fake da haukan karya don ta kubutar da 'yar ta mai suna Hassana.

Hamajiya ta jefa 'yar tata cikin wani rami mai zurfi a yayin da 'yan Boko Haram su ka surfafi garin su, Madagali, da ke Jihar Adamawa. Hamajiya ta rinka zurara ma Hassana abinci da ruwan sha cikin rami har na tsawon watanni 9.

Dabara: Dattijuwa ta shafe wata 9 tana haukan karya a hannun Boko Haram
Dabara: Dattijuwa ta shafe wata 9 tana haukan karya a hannun Boko Haram

Hassana ta cigaba da rayuwa cikin ramin har zuwa lokacin da Sojin Najeriya su ka fatattaki 'yan boko Haram daga garin. Ita kuwa Hamajiya, lokacin da 'yan Boko Haram su ka samu labarin ta na da 'ya budurwa, sai ta musanta kuma ta fake da haukan karya inda ta rika birgima a kasa kuma ta safe kanta da bayan gida duk dai domin su yarda bata da hankali.

DUBA WANNAN: Mutane 4 da ka iya bin sahun Atiku bayan ficewar sa daga APC

Tsananin azaba bai sa Hamajiya ta amsa tuhumar ba. Su kuwa Boko haram don tsoron ka da azabtar da mahaukaciya ya janyo masu wata mummunar kaddara, sai su ka hakura su ka rabu da ita.

Hauka ne tuburan Hamajiya ta daurawa kanta don dai ta tseratar da 'yar ta. Ita kuwa 'yar bayan Soji sun kubutar da garin na su, babu abun da ta ke yi sai godiya ga mahaifiyar ta bisa irin wannan tsabar soyayya da ta nuna mata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel