Dandalin Kannywood: Dalilin da yasa aure na ya mutu - Jaruma Asma'u Sani

Dandalin Kannywood: Dalilin da yasa aure na ya mutu - Jaruma Asma'u Sani

Fitacciyar jarumar nan ta wasannin fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood Hajiya Asma'u Sani ta fito tayi karin haske game da ainihin musabbabin dalin mutuwar auren ta a kwanan baya bayan ta shafe shekaru a gidan mijin nata.

Hajiya Asma'u da tayi tsokaci game da hakan a yayin wata fira da tayi da majiyar mu ta bayyana cewa mijin ta da aura a shekarun bayan ya yi zato ita wata hamshakiyar mai kudi ce musamman ma saboda yadda yaga tana fitowa amatsayin mace mai kudi a cikin fina-finan ta da dama.

Dandalin Kannywood: Dalilin da yasa aure na ya mutu - Jaruma Asma'u Sani
Dandalin Kannywood: Dalilin da yasa aure na ya mutu - Jaruma Asma'u Sani

KU KARANTA: Yadda 'yan sanda suka yi wa NafisaAbdullahi dirar mikiya a dakin ta na Otel

Legit.ng dai ta samu cewa sai dai a tun lokacin da ya gano ba haka lamarin yake ba, a cewar ta sai ya fara wulakanta ta yana ci mata mutunci daga baya kuma har yazo ya sake ta.

Daga nan ne ma kuma sai jarumar ta yi kira ga sauran al'ummar dake yi mata kallon kamar taki son zaman aure ne da su yi mata uzuri don kuwa ta matukar son aure don a cewar ta ko gobe idan ta samu miji zata sake yin aure domin shine suturan dukkan 'ya mace.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Online view pixel