Shugaban Kasar Egypt zai maida martani ga yan ta'addan da suka kai hari a masallaci

Shugaban Kasar Egypt zai maida martani ga yan ta'addan da suka kai hari a masallaci

- Shugaba Abdul Fattah Al-Sisi ya dauki alkawarin daukar fansa kan harin da yan ta'adda suka kai a masallacin Rawda

- Jim kadan bayan furucin shugaban, Sojin saman kasar sunyi luguden wuta kan wuraren da yan ta'addan ke ajiye makamai da alburusai

- Shugaban kasar ya ware kwanaki 3 domin zaman makoki ga wadanda suka rasu

Shugaban kasar Egypt Abdel Fattah al-Sisi ya lashi takobin daukar fansa kan wadanda suka kai hari a masallacin Rawda da ke yankin arewacin Sinai kuma suka hallaka mutane a kalla guda 235, wannan harin yana daga cikin mafi muni a tarihin kasar.

Zamu dau fansa kan mutanen da suka kai hari a masallaci - Shugaban Kasar Egypt
Zamu dau fansa kan mutanen da suka kai hari a masallaci - Shugaban Kasar Egypt

A sakon da shugaban kasar ya aike ta kafar talabijin yace zasuyi amfani da Jami'an yan sanda da Soji wajen daukar fansar shahidai da aka kashe musu, sannan zasu tabbatar da tsaro da zaman lafiya a kasar cikin lokaci kalilan.

DUBA WANNAN: Sarkin Kano ya zargi su babba da jaka bisa halin tabarbarewar arzikin Najeriya

Sa'o'i kadan bayan sakan shugaban kasar, Sojin sama na kasar sunyi luguden wuta kan wuraren da yan ta'addan ke ajiye makamai da alburusai, sojin sun kuma yi kaca-kaca da motocin da yan ta'adar sukayi amfani dashi wajen kai harin.

Al - Sisi ya ware kwanaki 3 na zaman makoki da zai fara daga ranar Asabar zuwa ranar Litinin.

Shugabanin kasashen duniya sunyi Allah wadai da harin. Shugaban kasar Amurka Donald Trump yayi amfani da shafinsa na Twita inda ya misalta harin a matsayin zalunci da ragwanci. Hakazalika, shima babban limanin birnin Cairo, Sheikh Ahmed el-Tayeb yayi tir da harin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel