Cau! Cau! Sa’a dai! Wasu mafarauta sun gwabza da yan ta’adda a Borno, sun hallaka guda

Cau! Cau! Sa’a dai! Wasu mafarauta sun gwabza da yan ta’adda a Borno, sun hallaka guda

Jami’in watsa labarai na rundunar Sojin Najeriya ya bayyana cewa wasu gungun mafarauta sun samu nasarar tarwatsa taron yan ta’addan Boko Haram, kamar yadda kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.

Kaakain rundunar, Birgediya SK Usman ya bayyan haka ne a ranar Juma’a 24 ga watan Nuwamba, inda yace mafarautan sun fito ne daga kauyen Gir ma karamar hukumar Biu, tare da taimakon mafarautan Damaturu.

KU KARANTA: Daki-daki yadda Atiku ya dinga sauyin sheka a tsakanin jam’iyyun Najeriya

Majiyar NAIJ.com ta bayyana cewa wannan arangama ya auku ne a dajin kauyen Burashika, duk a cikin garin Biu.

Cau! Cau! Sa’a dai! Wasu mafarauta sun gwabza da yan ta’adda a Borno, sun hallaka guda

Mafarauta

Bayan karanbattan, mafarautan sun kashe dan Boko Haram guda, tare da kwato bindiga guda daya, da alburusai da dama, haka zalika sun kwato Akuyoyi 58, tinkiya 36 da jakai 12.

Daga karshe SK Usman yace tuni sun mika dabbobin ga hannun jami’an tsaro dake kauyen Gur, a shirin gano masu su, don mika musu dabbobinsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar NAIJ.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Addu’a ne kadai zai iya kawo karshen ta’adanci a Najeriya - Yakubu Gowon

Addu’a ne kadai zai iya kawo karshen ta’adanci a Najeriya - Yakubu Gowon

Addu’a ne kadai zai iya kawo karshen ta’adanci a Najeriya - Yakubu Gowon
NAIJ.com
Mailfire view pixel