Neman Duniya: An kama Malamin addini da sashen jikin mutum a Ibadan

Neman Duniya: An kama Malamin addini da sashen jikin mutum a Ibadan

- ‘Yan Sanda sun kama wasu dauke da kan mutum

- Daga ciki wadanda aka kama har da wani Malami

- Malamin addinin yace neman dukiya ya jefa sa ciki

Yanzu haka mun ji labari a jiya cewa Jami’an ‘Yan Sandan Najeriya sun kama Malamin addini da wasu mutane 2 dauke da sashen jikin mutum a Garin Ibadan.

Neman Duniya: An kama Malamin addini da sashen jikin mutum a Ibadan
Saboda neman duniya wani Malamin addini ya fada halaka

Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Oyo Abiodun Odude ya tabbatar da wannan a jiya inda ya fito da wadannan mutane a gaban bainar Jama’a dauke da kai da kafafun mutune har 2. Kawo yanzu dai ba a fadi sunan wadannan masu laifi ba.

KU KARANTA: Shugaban EFCC Magu zai kafar wando daya da Jami'an DSS

Wannan Malami da aka kama da laifi ya furta da bakin sa cewa sun saci bangarorin mutanen ne a wata makabartar Musulmai da ke Ogbomosho. Neman dukiya ne dai ta sa wadannan mutane su ka shiga sace bangaren jikin gawa daga kabari.

Wannan Malami da aka kama da laifi ya bayyanawa manema labarai cewa wannan ne karon san a farko da yayi wannan danyen aiki. Wasu ne dai su ka fadawa Shehin yayi wannan aiki idan har yana so yayi kudi cikin gaggawa, shi kuma ya jarraba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel