Wallahi zan iya auren Maryam Sanda – Inji wani mutumi

Wallahi zan iya auren Maryam Sanda – Inji wani mutumi

Wani mutumi mai suna Comred-Zakari Y Adamu Kontagora ya bayyana cewa Idan har Maryyam Sanda, matar da ake zargi da hallaka mijinta tagama iddah, kuma ta gama fuskantar shari'a, tsaf zai iya auran ta kuma su zauna lafiya muddin ta ce tana son sa.

Shafin Rariya ce ta wallafa wannan labari inda ta rahoto matashin na cewa: “Idan har tagama iddah, kuma ta gama fuskantar shari'a, tsaf zan iya auran ta kuma muzauna lafiya muddin ta ce tana sona.”

Wallahi zan iya auren Maryam Sanda – Inji wani mutumi
Wallahi zan iya auren Maryam Sanda – Inji wani mutumi

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya shiyyar garin Abuja, babban birnin tarayya sun bayyana cewa sun samu faifan bidiyon ainihin abun da faru da har yayi sanadiyyar ajalin dan tsohon shugaban PDP Bilyaminu Bello da ake zargin matar sa Maryam Sanda da yi a gidan su.

Tun farko dai majiyar mu ta samu cewa matar ta sa ta caka masa wuka ne dai sau da yawa a cikin sa da kuma al'aurar sa bayan da ta zarge sa da shirin kara aure kafin daga bisani ya rasu.

KU KARANTA KUMA: Kisan Bilyamin: Yan sanda sun samu faifan bidiyon abun da ya faru, sun kama masu gadin gidan

Legit.ng dai ta samu cewa wani babba a rundunar 'yan sandan dai ya bayyana cewa sun samu faifan ne ta hanyar na'urar daukar hotunan sirrin nan ta CCTV kuma yanzu haka ma dai sun kama sauran masu gadin gidan da na'urar ta nuna suna taimakawa matar wajen daukar mijin zuwa cikin mota.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel