Ana amfani da bolar leda wajen yin bulo na zamani a Katsina

Ana amfani da bolar leda wajen yin bulo na zamani a Katsina

- Hukumar SEPA na Jihar katsina ta bullo da shirin amfani da ledar bola domin sarrafa bulo

- Hukumar tace wannan shirin zai taimaka wajen tsaftace Jihar da kuma samar da ayyukan yi har ma da bunkasa kudin shiga a Jihar

- Jami'in hukumar yayi ikirarin cewa bulo din da sukeyi da ledar bola tafi na siminti inganci

Hukumar kare muhalli na Jihar Katsina SEPA ta fara sarrafa ledoji da aka zubar a bola domin kera bulo na kawata gida da akafi sani a 'Interlocks' a turance.

Jami'in sashin bincike da cigaba na hukumar, Mista Rabiu Garba ne ya shaida wa hukumar samar da labarai na kasa NAN a ranar Talata a Katsina.

Ana amfani da ledar bola wajen yin bulo na zamani a Katsina
Ana amfani da ledar bola wajen yin bulo na zamani a Katsina

Garba yace wannan sabon shirin zai taimaka wajen rage yawan ledoji da ake zubarwa a garin wadanda suke yima muhalli ila wajen rage sinadiran da ke kasar, kuma zai rage barace-barace da yara sukeyi domin zasu samu sana'ar yi.

KU KARANTA: Yadda Diezani ta tilasta ma Jonathan ya sallame ni daga aiki - Stella Oduah

Ya kara da cewa hukumar tasu tana siyan kilogram 1 na ledar a kan Naira 25 bisa yanayin ledar kuma hukumar na siyan misalinm kilogram 500 a kullum duk da cewa na'urar su tana iya sarrafa fiye da hakan.

Jami'in yace hukumar ta SEPA zata bude rassa a Daura, Malumfashi, Dutsin-ma, Kankia da kuma Funtua domin a cewar sa bulo din interlocks da ake samar wa da leda yafi na Siminti inganci.

Daga karshe yace shirin zai taimkawa wajen samar da kudin shiga a Jihar da kuma tsaftace gari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel