Shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce sun kawo karshen daular Islama ta Iraqi

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce sun kawo karshen daular Islama ta Iraqi

- Shekaru ukku kenan ana ba-ta-kashi tsakanin yar ISIL da ta kafa sabuwar daular Islama

- Sauran musulmi na Duniya suka hada kai da Iran sun hambaras da ita

- Sun azabtar sun kashe sun zub da jini da sunan addinin Islama da jihadi

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce sun kawo karshen daular Islama ta Iraqi
Shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce sun kawo karshen daular Islama ta Iraqi

Shugaban Iran, kasar 'yan shi'a da ke gaba da Sunni na Saudiyya, ya saki bayani kan cewa a yanzu, sun yi galaba kan kungiyar Sunni masu jihadi a Syria da Iraki, masu kiran kansu ISIL, wadanda Boko Haram na Najeriya ke bi sau da kafa.

DUBA WANNAN: Ganduje ya gayyaci shekarau bude asibiti da Buhari yaki zuwa

An dai yi wa ISIL din taron dangi a duniya, inda aka murkushe su, aka kuma ruguje sabuwar daular tasu, shugabansyu kuma, wanda suna nada Khalifa, Abubakar Al-Baghdadi, ya tsere.

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce sun kawo karshen daular Islama ta Iraqi
Shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce sun kawo karshen daular Islama ta Iraqi

An kore su daga garuruwan da suka mamaye, suka kafa shari'ar Islama, a MOSUL da RAQQAH, inda suke bin tafarkin Sunna da Salaf tsantsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Iran dai yazuwa yanzu, ita ce kawai mai shugaba da za'a iya kira Limami ko Khalifa, su kuwa 'yan Sunna sai sarakuna.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel