Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya cika shekaru 60 a duniya a jiya. To sai dai wani abun mamaki da ya faru shine yadda yawancin 'yan uwan sa, abokan sa da sauran manyan yan kasuwa suka yi burus da shi a ranar zagayowar haihuwar tasa ba kamar a baya ba sadda yana mulki.

Cikin gaisuwa da kuma taya murnar zagayowar haihuwar da tsohon shugaban ya samu sun hada daga shugaba Buhari, jam'iyyar APC sai kuma tsohon shugaban majalisar dattijai David Mark.

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

KU KARANTA: Yan shi'a sun gargadi gwamnan Sokoto, Tambuwal

NAIJ.com dai ta samu cewa sai dai a wani yanayi mai ban mamaki, sai gashi kusan dukkan wadan da ada kan sayi warkoki da takardun jaridu don taya shi muranar zagayowar ranar haihuwar ta sa, a wannan shekarar duk sun yi fatali da shi din.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa irin hakan ta fara faruwa ga tsohon shugaban tun daga shekara biyu da ta wuce a 2015 jim kadan bayan da ya sha kaye a zabe.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Labari na musamman: Yadda wani ‘dan acaba ya kashe ‘Dalibar A.B.U

Labari na musamman: Yadda wani ‘dan acaba ya kashe ‘Dalibar A.B.U

Cikakken labari: Yadda wani ‘Dan acaba ya kashe ‘Dalibar A.B.U Zaria
NAIJ.com
Mailfire view pixel