A cikin jaruman Kannywood ina son inyi aiki tare da Rahama Sadau - Inji fitacciyar jarumar Nollywood

A cikin jaruman Kannywood ina son inyi aiki tare da Rahama Sadau - Inji fitacciyar jarumar Nollywood

Fittaciyar jarumar nan ta masana’antar shirya fina-finai na Kudu wato Nollywood, Linda Osifo ta bayyana aniyar yin wasa tare da korarriyar jarumar hausa Rahama Sadau.

A cewar jarumar, Rahama Sadau yar fim ce wanda ke cike da tarin basira da kuma kwarewa sosai a fannin shirya wasa.

Ta bayyana haka yayin da kai ziyara ta musamman da jaridar Pulse a makon da ya gabata.

Linda Osifo tace fitowar wasu jaruman kannywood a fina-finan nollywood yana taimaka wajen bunkasa masana'antar shirya fim na kasar baki daya.

A cikin jaruman Kannywood ina son inyi aiki tare da Rahama Sadau - Inji fitacciyar jarumar Nollywood
A cikin jaruman Kannywood ina son inyi aiki tare da Rahama Sadau - Inji fitacciyar jarumar Nollywood

Jarumar wanda tayi fice a fina-finai daban daban na dandalin nollywood tace hakika jaruman Kannywood na cike da basira kuma nan ba da dadewa tana fatan zata yi aiki da wasu daga cikin su.

KU KARANTA KUMA: Zaben Anambara: Babu wani abun mamaki a nasarar da Obiano ya samu – Shugaban jam’iyyar APGA, Oye

Linda wanda asali yar kabilar Ishan ce dake nan jihar Edo tace zata so ta koyi yaren hausa domin yana cikin yarurruka da take neman iyawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel