Zaben Anambara: Sanata Buruji Kashamu ya ba Makarfi laifi akan rashin kokarin PDP

Zaben Anambara: Sanata Buruji Kashamu ya ba Makarfi laifi akan rashin kokarin PDP

- Buruji Kashamu ya ce shugabancin Makarfi shine mafi muni a tarihin jam'iyyar PDP

- Sanatan ya ce Makarfi da abokan sa sun janyo jam'iyyar PDP bakin jini a Najeriya

- Sakamakon zaben gwamnan Anambara ya nuna PDP ne ta zo uku

Sanata mai wakiltar mazabar kudancin Ogun a majaliisar dattawa, Buruji Kashamu ya ba shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar PDP, Ahmed Makarfi, laifi akan rashin kokarin jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Anambara da aka gudanar a ranar Asabar.

Ya kuma ce yanayin shugabanci Makarfi shine mafi muni a tarihin jam’iyyar PDP.

Sanata Kashamau yace sakamakon zaben Anambara ya nuna Makarfi da mabiyansa sun janyo wa jam’iyyar PDP bakin jini.

Zaben Anambara : Senata Buruji Kashamu ya ba Makarfi laifi akan rashin kokarin PDP

Zaben Anambara : Senata Buruji Kashamu ya ba Makarfi laifi akan rashin kokarin PDP

“Ya za ayi ace jam’iyyar PDP ta zo na uku a zaben Anambara in ba rashin shugabanci ba.” Inji Kashamu.

KU KARANTA : Bankin Duniya ta amince ta ba El-Rufai bashin Dala miliyan $350

A ranar Lahdi 19 ga watan Oktoba hukumar zabe na INEC ta sanar da sakamakon zaben gwamna jihar Anambara inda dan takarar APGA ya yiwa sauran jam’iyyun fice, da kuri’o sama da dubu 200,00.

Jam’iyyar All progressive Congress APC ta zo na biyu sai jam’iyyar PDP ta zo na uku.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ma’aikatar ayyuka bata aiwatar da aiki ko daya ba a 2017 – Minista Fashola

Ma’aikatar ayyuka bata aiwatar da aiki ko daya ba a 2017 – Minista Fashola

Ma’aikatar ayyuka bata aiwatar da aiki ko daya ba a 2017 – Minista Fashola
NAIJ.com
Mailfire view pixel