Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da mamaci Cif Alex Ekwueme

Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da mamaci Cif Alex Ekwueme

Labaran da muke samu daga majiyoyin mu suna nuni da cewa tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya mai suna Alex Ekwueme ya mutu a wata asibiti dake can a birnin Landan jiya Lahadi, 19 ga watan Nuwamba.

NAIJ.com ta tattaro maku wasu muhimman al'amurra akalla 5 da ya kamata ku sani game da mamacin.

1. Cikakken sunan mamacin dai shine Cif Alex Ifeanyichukwu Ekwueme.

2. Yayi zama a matsayin mataimakin shugaban kasar Najeriya a karkashin mulkin Alhaji Shehu Shagari daga shekara ta 1979 zuwa 1983.

Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da mamaci Cif Alex Ekwueme

Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da mamaci Cif Alex Ekwueme

KU KARANTA: Kishi: Matar dan tsohon shugaban PDP ta kashe shi har lahira

3. An haifi mamacin ne dai a ranar 21 ga watan Oktoba shekarar 1932 sannan kuma ya mutu a 19 ga watan Nuwamba shekarar 2017. Ya mutu yana da shekaru 85 a duniya kenan.

4. Jam'iyyar da yayi itace National Party of Nigeria (NPN) sannan kuma kadan daga cikin makarantun da ya halarta sun hada da, King's College, Legas, jami'ar Washington, jami'ar Landan da dai sauran su.

5. Mamaci Alex fitaccen mai taswirar zane-zane ne. Sannan kuma ya fara aiki ne a matsayin mataimakin mai zane-zane na kamfanin Leo A. Daly and Associates dake a birnin Landan kafin daga bisani ya dawo Najeriya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain NAIJ.com HAUSA

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ma’aikatar ayyuka bata aiwatar da aiki ko daya ba a 2017 – Minista Fashola

Ma’aikatar ayyuka bata aiwatar da aiki ko daya ba a 2017 – Minista Fashola

Ma’aikatar ayyuka bata aiwatar da aiki ko daya ba a 2017 – Minista Fashola
NAIJ.com
Mailfire view pixel