Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alex Ekueme ya mutu a Landan

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alex Ekueme ya mutu a Landan

Labaran da muke samu suna nuni da cewa tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma mai rike da sarautar gargajiya ta Oko a jihar Anambra mai suna Alex Ekwueme ya mutu a wata asibiti can birnin Landan jiya Lahadi, 19 ga watan Nuwamba.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da iyalan sa suka fitar dauke da sa hannun kanin sa a cikin daren jiyan inda ya bayyana rashin a matsayin babba a gare su dama sauran 'yan Najeriya a duk inda suke.

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alex Ekueme ya mutu a Landan

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alex Ekueme ya mutu a Landan

KU KARANTA: Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku yayi ganawa ta musamman da Shekarau

NAIJ.com dai ta samu cewa kanin nasa a cikin sanarwar ya bayyana cewa mamacin ya mutu ne da kimanin karfe 10 cif na daren jiya Lahadin a asibitin da yake jinya.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa Cif Alex Ekwueme a kwanan baya ya fadi a some a gidan sa dake can Enugu a cikin watan da ya gabata inda daga bisani aka kwashe shi zuwa asibitin waje domin jinyar sa.

Haka ma dai mamacin ya mutu ne yana da shekaru 85 a duniya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain NAIJ.com HAUSA

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-yanzu: Rikici a gidan Kwankwasiyya, Farfesa Hafiz yayi fito-na-fito da Kwankwaso, zai yi takaran gwamna

NAIJ.com
Mailfire view pixel