Tunawa da gwani: Ka san wanene Mahaifin Bukola Saraki?

Tunawa da gwani: Ka san wanene Mahaifin Bukola Saraki?

- Mahaifin Bukola Saraki rikakken ‘Dan siyasa ne

- Tafiyar Mahaifin da ta ‘dan sa tayi kama da juna

- Olusola Saraki ya zama Sanata a lokacin Shagari

Jama’a da dama ba su da labarin Mahaifin Bukola Saraki watau Marigayi Olusola Saraki wanda yayi siyasar a lokacin Jamhuriyya ta biyu watau 1978-1983. Kwanan nan Bukola Saraki yayi makokin shekaru 5 na rashin mahaifin na sa. Saraki ya rasu a Nuwamban 2012.

Tunawa da gwani: Ka san wanene Mahaifin Bukola Saraki?
Olusola Saraki: Kusa a lokacin siyasar Jamhuriya ta 2

Tafiyar siyasar Mahaifin Shugaban Majalisar Dattawan Kasar da ta Mahaifin na sa tayi kama da juna don kuwa Olusola Saraki ya rike Shugaban masu rinjaye a Majalisar Datawa lokacin Shugaban Kasa Shehu Shagari kafin Gwamnatin Buhari ta hambarar da su.

KU KARANTA: Bukola Saraki ba zai nemi takara ba a zaben 2019

Haka kuma Olusola Saraki yayi yunkurin zama Shugaban kasa amma bai samu tsallake zaben fitar da gwani ba na Jam’iyyar NPN. Shi ma dai Bukola Saraki ya dade yana neman tsayawa takara Shugaban Kasa amma ta kai dole ya hakura ya janye ya nemi kujerar Sanatan sa.

Ana dai ganin Mahaifin Saraki yana cikin wadanda su ka rika juya harkar siyasar Jihar Kwara wanda a yanzu kuma Bukola Saraki ne ke da akalar siyasar Jihar. Wasu ma na gani shi ma yanzu yana kokarin ganin ‘dan sa ya samu mulki ko da cewa ya karyata wannan labari.

Olusola Saraki dai Likita ne da yayi karatu a Makarantar St George’s Hospital Medical School da ke Landan. Shi ma Bukola Saraki ya karanta Likitanci ne a Landan amma ya shige harkar siyasa. ‘Yar uwar sa Gbemisola Saraki tsohuwar Sanata ce kuma har gobe ana damawa da ita.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel