Matsalar shaye-shaye 'yan mata da samari a arewa ta kai Innaa-Lillahi

Matsalar shaye-shaye 'yan mata da samari a arewa ta kai Innaa-Lillahi

A duk duniya a yau, babu inda ya kai arewacin Najeriya musamman jihar Kano, yawan masu shan Codeine, wani maganin tari mai sanya mutum bacci. Masu bincike sun tabbatar wannan yana da alaka da halayyar jama'ar Arewa dake haifar wa da 'yan mata da matan aure damuwa da rashin abin yi.

Matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi da kayan maye ta zama ruwan dare a arewacin Najeriya musamman a jihar Kano.

Bincike ya nuna lallai da yawan masu shan kayan mayen nan suna yi ne don su yaye wa kan su bakin ciki ko damuwa da suke tsintar kan su a ciki.

Matsalar shaye-shaye 'yan mata da samari a arewa ta kai Innaa-Lillahi
Matsalar shaye-shaye 'yan mata da samari a arewa ta kai Innaa-Lillahi

Sabon salon da ya fito, mata kuma ke yayi, shine shan Codeine da Rafanol da ma Benylin da sauran miyagun kwayoyi.

DUBA WANNAN: An yankewa Trump hukuncin kisa a Koriya ta Arewa

Matsalar shaye-shaye 'yan mata da samari a arewa ta kai Innaa-Lillahi
Matsalar shaye-shaye 'yan mata da samari a arewa ta kai Innaa-Lillahi

Hoto daga jaridar DailyTrust

Abin tada hankali shi ne yadda 'yan mata suke shiga irin wannan mummunar dabi'a. Tun daga fatauci da sayarwa har zuwa shaye-shayen miyagun kwayoyin.

Yin hakan ba karamar illa yake ga jikin dan adam ba, yana lalata hanta da koda a jikin mutum har ya kai ga rayuwar mutum ta salwanta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Da yawan mata suna shiga wannan mummunan dabi’ar ne ko kuma su dinga yawo Otal bin samari, kuma sama da rabin mashayan kwayoyin mata ne. Wasu kuma da yawan su masu sayan kayan mayaen matan aure ne masu fama da bakin cikin zamantakewar aure, suna shan kwayoyin ne saboda su dauke hankalinsu daga damuwar da suke ciki.

Da yawan su suna shan Codeine dinne saboda ya yaye musu bakin ciki da damuwa, yadda wata matar ta shaidawa gidan jaridar BBC ta fara sha ne bayan mutuwar aurenta.

Wasu kuma ‘yan matan suna shan kwayoyin ne saboda su yaye wa kan su damuwa, wata da aka gana da ita ta shaida cewa tana shan kwayar ne domin ta yaye bakin cikin da ta shiga saboda saurayinta ya rabu da ita.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel