Babbar kotun Koriya ta Arewa ta yankewa shugaban Amurka Donald Trump hukuncin kisa

Babbar kotun Koriya ta Arewa ta yankewa shugaban Amurka Donald Trump hukuncin kisa

- Kiransa dan lukuti mai roka da shugaban Amurka yayi ya kona masa rai

- Shuwagabannin biyu sun raina juna

- Kiris ya rage ma Amurkar ta afkawa Koriyar da yaki, sai aka baiwa Trump baki

Dramar kasashen Asiya da Amurka bata karewa, domin kuwa a makon nan ne kotun Koriya ta Arewa ta yankewa shugaba Trump na Amurka hukuncin kisa.

Babbar kotun Koriya ta Arewa ta yankewa shugaban Amurka Donald Trump hukuncin kisa
Babbar kotun Koriya ta Arewa ta yankewa shugaban Amurka Donald Trump hukuncin kisa

Tayi hakan ne bayan da ya zagi shugaban kasar saboda shisshiginshi da kokarin sai ya mallaki manyan makamai da aka haramtawa talakawan kasashe.

Su dai Amurka da kawayenta sun mallaki makaman Nukiliya da na guba da ma masu yada cututtuka, amma sun hana kowa ya tanada.

DUBA WANNAN: Hoton fuskar Annabi isa ya sayu a dala miliyan dari hudu

Shi kuwa shugaban Koriya ya dage sai ya mallaki wadannan makamai, don haka ake hararar juna tsakaninsu da Amurka, kuma a taron majalisar dinkin duniya, Trump ya kira shi da dan lukuti mai roka, dama ce masa yaro mai giggiwa, ashe abin ya harzuka shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

A kasarsa di, hukuncin kisa ne idan aka zage shi ko iyalinsa, domin haka wata kotu ta dauki wannan korafi ta shigar kara, nan take kuwa aka sami hukunci; hukuncin kisa a kan Donald Trump na Amurka.

Sai dai ba'a san yadda suke shirin dauko shi daga Amurka don rataya ba, domin Amurka ta fi su karfin soji ninkin ba-ninkin.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel