Rana dubu ta barawo: An kama masu garkuwa da mutanen da suka addabi Sabon Gayan a Kaduna

Rana dubu ta barawo: An kama masu garkuwa da mutanen da suka addabi Sabon Gayan a Kaduna

- Sune suka kashe shugaban matasa na garin, wanda ya janyi uban go-slo a hanyar Abuja a ranar Lahadi

- Gurgu ne mai musu leken asiri

- 'Yan sanda sun ceto mutane uku da suka sace

'Yan sandan jihar Kaduna sun zaga gari kowa-ya-gani da wasu 'yan fashin da suka kama su tara, wadanda ake zargin su da yin fashi, satar mutane, kwacen mota da sayar da hodar Iblis.

Mai magana da yawun bakin 'yan sandan jihar, CSP Jimoh Moshood, ne ya baiyanawa manema labarai haka. Yace an kama su ne a garin Sabon Gayan, da ke jihar.

Wasu daga cikin masu garkuwa da mutanen da aka kama
Wasu daga cikin masu garkuwa da mutanen da aka kama

'Yan fashin su ne: Umaru Ibrahim Mujuma (Shugaban su), Jibrin Adamu, Samaila Haruna, Ibrahim Mohammed, Ibrahim Idris, Iliya Adamu, Ifeanyi Linus, Silas Kelvin (mai yi musu cinikin satattun motoci da kuma sayar da hodar Iblis) da kuma Kamilu Mohammed (wanda gurgu ne amma shine mai leken asirin su).

Wasu daga cikin masu garkuwa da mutanen da aka kama
Wasu daga cikin masu garkuwa da mutanen da aka kama

Yan sanda sun kwaci makamai a hannun su wanda sun hada da bindigogi da harsasai, da kuma motoci guda biyu kirar Toyota Corolla.

Motocin da aka kama a hannun 'yan fashin
Motocin da aka kama a hannun 'yan fashin

Bayan kisan gillar da aka yi wa shugaban matasa Haruna Maikudi Maikaji a gonar sa da ke Sabon Gayan a ranar 12 Oktoba, Sifeto Janar na 'yan sanda, Ibrahim Idris, ya jajinta wa iyalin sa da mazauna garin, kuma ya sha musu alwashin binciken kamo wadanda suka aikata wannan katobarar don su fuskanci hukuma.

Kowa-ya-shaida: Masu garkuwa da mutanen da aka kama
Kowa-ya-shaida: Masu garkuwa da mutanen da aka kama

Ya aika da kwararrun dakaru na Ofereshin Absolut Saniti don su tsefe garin su nemo 'yan daban. A cikin binciken su ne sai 'yan fashin suka sumami dakarun suka afka musu. Labari ya zo mana cewa Kamilu Gurgu ne ya kai wa 'yan fashi labarin inda dakarun suka yi sansani.

Fada ko ya barke tsakanin su har dakarun suka samu suka bindige 'yan daba 2 har lahira. Mutum daya kuma daga cikin dakarun ya sami mummunan rauni, wanda a yanzu haka yana asibiti.

'Yan kallo a wurin da 'yan sanda suka zaga da 'yan fashin
'Yan kallo a wurin da 'yan sanda suka zaga da 'yan fashin

Wadanda aka damke a nan sun baiyana maboyar su kuma da wanda ya kawo musu labarin (Kamilu gurgu). Yan sanda sun je sun yi awon gaba da shi kafin su durfafi gidan 'yan fashin.

Sun fatattaki mazauna gidan sun kame su. Sun kuma yi kicibis da wadansu mutane uku da aka yi garkuwa da su, wadanda ba'a baiyana suna su ba, da 'yan fashin suke jira iyalan su su biya kudi.

Mutanen da aka ceto sun nuna 'yan fashin da suka aikata musu wannan aika-aikar.

DUBA WANNAN: Kaso 75 na 'yan Najeriya na amfani da yanar gizo - Minista

Moshood ya ce ana nan ana ci gaba da bincike, amma duk wadanda aka kama har sun riga da sun amsa laifuffukan su. Ya ce ana gama bincike za'a dunguma da su gaban hukuma.

Shugaban 'yan sanda na kasa ya jinjina wa wadannan 'yan sanda kuma ya bada oda cewa kowace gabar 'yan sanda ta jiha ta gyara damara don ta shiga binciken makwantar 'yan fashin jihohin ta don a gyara kasa baki daya. Ya ce musamman kuma ga shi an kusa fara tafiya hutun Kirsimeti.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:

labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel