A daina amfani da kwayar maganin ‘Antibiotics’ ba tare da izinin likita ba

A daina amfani da kwayar maganin ‘Antibiotics’ ba tare da izinin likita ba

- Likitoci sun gargadi mara sa lafiyan dake amfanin da antibiotics ba tare da izini ba

- Likitoci sun ce yazama dole mara lafiya ya nemi izinin likita kafin ya fara amfanin da kwayar maganin Anti Biotics

- Tsaftace muhalli shine garkuwa ga kowani irin ciwo inji likitoci

Antibiotic maganin da ke warkar da cutar ke dauke da karamin halitta mai suna Bacteriya.

Likitoci sun koka akan yadda Mutane suke amfani da magagunan antibiotcis ba tare da izinin likita ba, wanda yasa maganin ya daina aiki a jikin wasu saboda yadda su ke amfani da shi ba a bisa ka’aida ba.

A daina amfani da kwayar maganin ‘Antibiotics’ ba tare da izinin likita ba
A daina amfani da kwayar maganin ‘Antibiotics’ ba tare da izinin likita ba

Kungiyar kula da kiwon lafiya na duniya WHO ta bayyana abubuwa guda shida 6 da mutane ya ka mata su sani game da maganin Anti Biotics.

KU KARANTA : 2019 : APC ta yi magana akan ra’ayin Orji Kalu na son tsayawa takarar shugaban kasa

1. Yazama dole mara lafiya ya nemi izinin likita kafin ya fara amfanin da kwayar maganin Anti Biotics.

2. Kwayar maganin ‘Antibiotics’ ba ya maganin cutar ‘Virus’ kamar tari, mura, atishawa da sauran su.

3. Rika tsafatace muhalli da wajen zama, wanda shine babbar kariya ga kowani irin cuta..

4. Mara lafiya ya tabbatar da yayi amfani da maganin kan cutar da yakamata.

5. Kuma a sha adadin kwaoyiyn da likita ya umarci mara lafiya sha.

6. Kuma a daina ba dabbobi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel