Farida Waziri makaryaciya ce - Inji Jonathan

Farida Waziri makaryaciya ce - Inji Jonathan

- Jonathan yayi raddi ga tsohuwar shugaban hukumar EFCC

- Ya bayyana zargin da ta yi masa a matsayin karya

- Tsohon shugaban kasar ya bayyana Farida a matsayin sojar haya

Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, ya yi raddi akan zargin da tsohuwar shugabar hukumar dake yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa wato EFCC, Farida ta yi masa na cewa shi ya daure gindin yadda aka rika wawurar kudade a lokacin mulkin sa.

Wadannan furuci na tsohuwar shugabar ta EFCC ba su yi wa tsohon shugaba Jonathan dadi ba, inda ya shiga shafin sa na Twitter a ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba ya caccaki Farida Waziri.

Ya na mai cewa: “Idan Farida ba karya ta ke fada ba, ai sai ta fito ta bayyana sunan mutumi ko kamfanin da ta ce na hana ta bincika.”

Farida Waziri makaryaciya ce - Inji Jonathan
Farida Waziri makaryaciya ce - Inji Jonathan

Jonathan ya ci gaba da da zargin cewa dauko Farida akayi a matsayin sojar-haya, saboda ta tozarta shi.

KU KARANTA KUMA: Rikici ya barke a Jam’iyyar ‘Labour Party’ ana shirin zaben Gwamna

Tsohon shugaban kasar dai na ci gaba da shan adawa tun bayan da ya fadi a zaben 2015, inda ake dora masa laifin bari aka rika wawurar kudaden Najeriya.

Tun yana kan karagar mulki ya kare gwamnatin sa, tare da cewa masu sukar gwamnatin ba su kallon alherin da ya shuka, sai matsalolin ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel