Dangote ya miƙa ma kungiyar mata wani katafaren Masallacin naira miliyan 100

Dangote ya miƙa ma kungiyar mata wani katafaren Masallacin naira miliyan 100

Kasaitaccen Attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote ya kammala ginin wani katafaren Masallaci da aka kashe naira miliyan 100 wajen gina shi a garin Abuja, sa’annan ya mika shi ga kungiyar mata Musulmai, FOMWAN.

Kaakakin gidauniyar, Anthony Chiejina ne ya bayyana haka cikin wata sanarwar daya fitar a ranar Laraba 15 ga watan Nuwamaba a garin Abuja, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: Sauƙi ya samu ga Malamai 22,000 da El-Rufai zai kora, wani hamshaƙin ɗan kasuwa zai basu aiki

Anthony yace giduaniyar Dangote ta dauki gabaran cigaba da ginin Masallacin ne dake Utako bayan neman agaji da kungiyar FOMWAN tayi ga Alhaji ALiko Dangote, inda yace a yanzu haka an mika Masallacin ga shugaban FOMWAN, Hajiya Amina Omoti.

Dangote ya miƙa ma kungiyar mata wani katafaren Masallacin naira miliyan 100
Yayin miƙa Masallacin

Jami’in daya wakilci gidauniyar a yayin mika Masallacin, Bala Usman yace Dangote ya gina Masallacin ne da nufin taimakaon jama’an yankin, ta hanyar sama musu da kasaitaccen Masallacin don ibada.

A nata jawabin, shugaban kungiyar, Omoti, ta yaba ma gidauniyar tare da gode ma mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar, sa’annan tace za’a gudanar da bikin bude masallacin a watan Janairun shekarar 2018.

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel