Jiragen ruwan yakin Amurka 3 sun isa tekun Koriya

Jiragen ruwan yakin Amurka 3 sun isa tekun Koriya

Rahotanni sun kawo cewa kasar Amurka ta fitar da bidiyon jiragen ruwanta na yaki 3 da suka isa gabar tekun kasar Koriya ta Arewa.

An dai fitar da faifan bidiyonne ta shafin Youtube mallakar rundunar sojin ruwan Amurka.

Bayanai sun nuna cewa, jiragen sun isa yankin ne domin gudanar da atisaye tare da sojojin Koriya ta Kudu.

Kafafan yada labaran kasar sun ce, a karon farko jiragen ruwa na yaki samfurin USS Ronald Reagan, USS Nimitz da USS Theodore Roosevelt sun yi shawagi a karon farko.

KU KARANTA KUMA: Yayinda Muhammadu Buhari ke Anambra, Osinbajo ya jagoranci zaman majalisa (hotuna)

Akwai kuma wasu karin jiragen ruwa 10 da suka hada da Sejong the Great da the Seoae Yu Seong-ryong da suke rakiya ga manyan jiragen ruwan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel