Dandalin Kannywood: Burin mu samar wa 'yan fim irin martabar malamai da sarakuna - Wata kungiyar fim

Dandalin Kannywood: Burin mu samar wa 'yan fim irin martabar malamai da sarakuna - Wata kungiyar fim

Wasu gungun matan dake sana'ar fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood a karkashin inuwar kungiyar da suka sa wa suna 'Kannywood Celebrities' sun fito sun bayyanawa duniya babban burin su a rayuwa musamman ma dai a bangaren da ya shafi sana'ar su ta fim.

Gamayyar kungiyar jaruman mata dai sun bayyana cewa a yanzu haka su ba su da burin da ya wuce su samar wa 'yan fim din musamman ma mata daraja dai-dai da malamai da kuma sarakuna a masana'antar ta su.

Dandalin Kannywood: Burin mu samar wa 'yan fim irin martabar malamai da sarakuna - Wata kungiyar fim
Dandalin Kannywood: Burin mu samar wa 'yan fim irin martabar malamai da sarakuna - Wata kungiyar fim

KU KARANTA: Wata mata ta haihu kwana 1 bayan auren ta a Katsina

Legit.ng dai ta samu daga majiyar ta mu cewa matan sun kuma ta bayar da yakinin cewa tabbas zata cimma burin ta domin kuwa dama can shine matsayin da ya dace da su musamman ma dai idan akayi la'akari da irin gudummuwar da suke bayarwa ga al'umma wajen ilmantar wa da nishadantarwa.

A baya ma dai mun kawo maku cewar fitacciyar jarumar nan ta wasan fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood kuma 'yar asalin jihar Kano mai suna A'isha Aliyu da ake yi wa lakani da A'isha Tsamiya ta bayyana dalilin da ya sanya ita bata saka kananan kaya kamar sauran wasu jaruman inda tace basu yi mata kyau ne.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Online view pixel