Shirin shugaba Buhari na N-power shiririta ce kawai - Adeyanju

Shirin shugaba Buhari na N-power shiririta ce kawai - Adeyanju

Shugaban wata kungiyar 'yan kishin Najeriya, Deji Adeyanju, ya bayyana shirin nan na samar da aiki ga na N-power, karkashin gwamnatin shugaba Buhari, a matsayin shiririta.

Da yake bayyana ra'ayin sa a wani shiri da gidan talabijin na Channels ke gabatarwa kullum, Adeyanju, ya ce rage radadin talauci ba daya yake da samar da aiki ba.

Shirin shugaba Buhari na N-power shiririta ce kawai - Adeyanju

Deji Adeyanju

Hakazalika, Adeyanju, wanda ya a baya ya taba rike mukamin darektan sadarwar zamani na jam'iyyar PDP ya zargi shugaba Buhari da yin makarkashiya ga kasuwancin wadanda keda burin yin takarar shugabancin kasa a zabe mai zuwa.

DUBA WANNAN: Buhari ya sha ruwan sarautu a wurin sarakunan kabilar Igbo

"Ban ga takamaimai aikin da shirin na N-power ya samar ba" a kalaman Adeyanju.

Adeyanju ya baiwa gwamnatin shugaba Buhari shawarar ta mayar da hankali wajen koyar da matsa sana'o'in dogaro da kai ta hanyar basu horo karkashin kulawar bankin kula da harkokin masana'antu ba wai ba wa matasa marasa aiki kudin kashewa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarki Sanusi II ya caccaki ministocin Buhari

Sarki Sanusi II ya caccaki ministocin Buhari

Sarki Sanusi II ya caccaki ministocin Buhari
NAIJ.com
Mailfire view pixel