'Yan kasuwa sun zubar da hawaye yayin da gobara ta kama shaguna a birnin Akure

'Yan kasuwa sun zubar da hawaye yayin da gobara ta kama shaguna a birnin Akure

Dukiyoyi na miliyoyin naira sun salwanta yayin da gobara ta kama shaguna 14 a babban jihar Ondo na Akure.

A ranar Talatar da ta gabata ne 'yan kasuwar suka rinka zubar da hawaye yayin da suke bayyana irin asarar da suka tafka sakamakon wannan gobara da afku da misalin karfe 2:00 na dare a babbar hanyar Roadblock dake daura da wurin sayar da abinci na Chicken Republic.

'Yan kasuwa sun zubar da hawaye yayin da gobara ta kama shaguna a birnin Akure

'Yan kasuwa sun zubar da hawaye yayin da gobara ta kama shaguna a birnin Akure

NAIJ.com ta ruwaito da sanadin jaridar Daily Trust cewa, wannan gobara ta afku ne sakamakon wata 'yar matsala ta wutar lantarki, inda mazauna yankin suka yi iyaka bakin kokarin su na kashe wutar bayan ta debi awanni tana aika-aika a shagunan kafin zuwan 'yan kwana-kwana.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: An gwabza tsakanin mambobin jam'iyyar APGA da APC a jihar Anambra

Dukiyoyi na tarin miliyoyi sun salwanta a cikin shagunan da wannan gobara ta lashe, inda 'yan kasuwar suka bayyana cewa mafi akasarin hajojin su sababbi ne da suke shirin cin kasuwar bikin kirsimeti da kuma sabuwar shekara.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200

Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200

Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200
NAIJ.com
Mailfire view pixel