Budadiyar wasika zuwa ga makiyana - Adam A Zango

Budadiyar wasika zuwa ga makiyana - Adam A Zango

- Adam A zango ya rubuta wa mutanen da suke suke masa karya da kazafi budadiyar wasika

- Shahararren dan wasan kwaikwayon ya nemi gafarar masoyan sa akan budadiyar wasikar da ya rubuta wa makiyan sa

- Zango yayi alkwarin tona asirin masu masa kazafi idan basu tuba sun daina ba

Shahararren dan wasan kwaikwayo da waka na kamfanin Kannywood Adam A Zango ya rubuta budadiyar wasika zuwa ga makiyin sa.

Adama a Zango ya rubuta wannan wasika ne a shafin sa na sa da zumunta na Instgaram.

Inda shaharraren mawakin ya koka akan yadda makiyan sa suke masa karya da kazafi wajen siffanta da wasu munana halaye.

Budadiyar wasika zuwa ga makiyana - Adam A Zango
Budadiyar wasika zuwa ga makiyana - Adam A Zango

Adam A Zango ya rubuta wasikar a shafin sa na Instagaram kamar haka.

KU KARANTA : Dandalin Kannywood: Dalilin da yasa bana sanya kananan kaya - Jaruma Aisha Tsamiya

BUDADDIYAR WASIKA IZUWA GA MAQIYANA

Ni ba dan daudu bane kuma ni ba dan maula bane. Sannan ni ba mushiriki bane, bani da malami ko matsafi.

Da ALLAH kadai na dogara. Idan kuma akwai malamin da yace na taba zuwa wajansa ko kuma wanda ya taba bani kudi kyauta ba tare da nayi masa aikin komai ba, toh dan girman ALLAH kada ya rufa min asiri tun daga kan yan siyasa, sarakuna, gwamnati, ko masu kudi, ko yammata…. duk abinda dana mallaka a rayuwata gumi na ne ya bani ba dan adam ba…motar hawa, gida ko fili….

Don haka babu wanda ya isa ya sani inyi abinda banyi niyya ba tunda babu wanda ya tayani kare mutuncin daukakata.

DON HAKA TA HANYA DAYA KADAI ZAKU IYA DAKATAR DA DAUKAKATA……HANYAR ITACE KU DAKATAR DA NUMFASHINA, SAI DAI KUMA KASH HAKAN BA’A HANNUNKU YAKE….HABA KUYI TA YAWO DANI KUNA BATA MIN SUNA DON KAWAI ALLAH YA FIFITANI AKANKU.

Kun ce min arne kunce min gay kunce min fasiki kunce min mai girman kai amma duk da haka masoyana basu gujeni ba basu daina sayan fina finai da wakokina ba. Haba don ALLAH mai nayi muku duk wanda na taimaka a rayuwata sai ya dawo yana yakata!! Toh na kai bango……

Billahillazi la’ila ha illahuwa duk wanda ya kara kara tabani saina tona masa asiri. Sannan duk wanda ya rufa min asiri akan abubuwan dana lissafa ALLAH ya tona masa nasa. Ban kira sunan kowa ba a yanzu amma next time zan kira sunan ko waye idan ya kara bata min suna ….ina da ýaýa ya zama dole in fara kare mutuncina da martaba na kafin yayi affecting dinsu don ALLAH kadai ya san gawar fari….sannan zanja tunga da mabiyana na kannywood…. don a haka ne kadai za’a bam bance tsakanin aya da tsakuwa….

MASOYANA KU GAFARCE AKAN ABUBUWAN DANA RUBUTA, AN KURE NI NE”

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku ci gaba da bin mu a

Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa

Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Online view pixel