Dandalin Kannywood: Dalilin da yasa na fara fim din barkwanci - Ali Nuhu

Dandalin Kannywood: Dalilin da yasa na fara fim din barkwanci - Ali Nuhu

Fitaccen jarumin nan, mai bayar da umurni, mai shiryawa da kuma koyar da rawa a masana'antar fina-finan Hausa da ya dade yana haskakawa ya fito ya bayyanawa duniya dalilin da yasa yanzu ya tsunduma sosai cikin harkar fina-finan barkwanci da a da ba kasafai yake yin su ba.

Jarumin dai ya bayyana cewa ya yanke shawarar yin hakan ne domin ya fito ya bayar da gudummuwar sa a wannan bangaren sannan kuma ya sake fuskantar wani sabon kalubalen don kuwa ya gaji da yadda ya dauki tsawon lokaci yana fitowa a matsayin saurayi yana ta tikar rawa.

Dandalin Kannywood: Dalilin da yasa na fara fim din barkwanci - Ali Nuhu
Dandalin Kannywood: Dalilin da yasa na fara fim din barkwanci - Ali Nuhu

KU KARANTA: Yadda wani ma'aikacin jinya ya kashe mutane 100

Legit.ng dai ta samu cewa jarumin yayi wannan karin hasken ne a yayin da yake wata fira da tashar tauraron dan adam din nan ta Arewa24 a cikin satin da ya gabata a yayin da ake daukar shirin nan nasu na Kundin Kannywood.

Haka zalika ma dai jarumin ya musanta zargin cewa sun kanannade harkar fim din inda sukan hana sabbin fuskoki fitowa domin su taka irin tasu rawar inda ya bayyana cewa masana'antar shirya fim din tana da fadin gaske da wani ba zai iya tarewa wani wurin sa ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Online view pixel