Na shiga halwa, kuma na samu wahayi akan zaɓen 2019, an umarce ni in sake tsayawa takara – Inji Gwmanan jihar Benuwe

Na shiga halwa, kuma na samu wahayi akan zaɓen 2019, an umarce ni in sake tsayawa takara – Inji Gwmanan jihar Benuwe

Yayin da zabukan shekarar 2019 ke karatowa, yan siyasa da masu rike da madafan iko na cigaba da neman hanyoyi da zasu cigaba da darewa akan mukamansu, don haka zasu bi duk hanyar data dace da bukatarsa.

A nan ma wani gwamna ne daga cikin gwamnonin jihohin Arewa, gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwe ya bayyana cewa ya samu wahayi, inda aka umarce shi daya sake tsayawa takara a shekarar 2019.

KU KARANTA: Wani Ɗan-Daudu dake yaudarar samari ya shiga hannu a garin MInna, kalli yadda aka kwashe

Gwamna Ortom yace ya samu wannan wahayi ne bayan ya shiga halwa, inda yayi azumi, kuma ya gudanar da addu’o’i, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Na shiga halwa, kuma na samu wahayi akan zaɓen 2019, an umarce ni in sake tsayawa takara – Inji Gwmanan jihar Benuwe
Gwmanan jihar Benuwe

Ortom ya bayyana haka ne ga jama’an yankin Masev, Iharev da Nongov da suka kai masa ziyara, inda yace musu a yanzu kam ya shirya tsaf don sake neman kuri’un jama’an jihar don zama gwamna a karo na biyu.

Gwamna ya kara da rokan jama’an da suka kai masa ziyara, kan su ja kunnen duk wani dan kabilarsu dake da muradin takarar gwamna daya hakura, kuma yazo su hada hannu da shi don ciyar da jihar gaba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito an taba tambayar gwamnan ko zai tsaya takara a raanr 11 ga watan Satumba, inda yace bai shirya ba, kuma bashi da wata masaniya har sai yayi azumi.

“A yanzu ban fara addu’a ba, zan fara yin addu’o’i daga karshen shekarar nan.” Inji Ortom a wancan lokaci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel