Yadda ciyaman din karamar hukuma da kansiloli su ka ci mutumcin 'Yan majalisar jihar Neja

Yadda ciyaman din karamar hukuma da kansiloli su ka ci mutumcin 'Yan majalisar jihar Neja

- Rikci ya barke ne tsakanin yan majalisan jihar da shugabanin kananan hukumomi a dalilin kwangilar gina titi

- Yan majalisan sunyi yunkurin dakatar da aikin titin ne bayan sun lura cewa yan kwangilan sun saba alkawuran da akayi dasu

- Hakan kuma baiyi wa shugabanin kananan hukumomin dadi ba har yasa sukayi zage-zage da ma jifan yan majalisan

A ranar Alhamis ne Majalisar Jihar Neja ta dakatar da zababbun Ciyaman da Kansilolin Karamar Hukumar Mashegu saboda rashin ladabi. Hakan ya biyo bayan rahoton da Majalisar ta bukata ne daga bakin Kwamitin ta mai kula da harkokin Kananan Hukumomi.

Don haka ne Shugaban Kwamitin, Abdulmalik Kabir ya bayyana yadda masu gina titin da ke tsakanin Kawo da Mashegu su ka bijirewa yarjejeniyar tsarin da a ka yi magana a kai, a kan kudi naira miliyan 386. Sun ki yin magudanan ruwa sun kuma yi cogen fadi har na mita 1.9 a wasu wuraren.

Yadda Ciyaman din Karamar Hukuma da Kansiloli su ka ci mutumcin 'Yan Majalisar Jihar Neja
Yadda Ciyaman din Karamar Hukuma da Kansiloli su ka ci mutumcin 'Yan Majalisar Jihar Neja

Bisa haka ne Kabir ya bukaci a sa dan kwangilan aikin, ya koma ya yi gyare-gyare kamar yadda a ka tsara. Nan ne fa Ciyaman din Karamar Hukumar ya kada baki ya ce ai 'Yan Majalisun ne su ka umurci a dakatar da aikin ba shi ba, alhali kudin ba na su ba ne.

DUBA WANNAN: Kungiyar CAN ta bukaci Najeriya ta fita daga Kungiyar musulunci ta OI

Kabir ya ce daga nan ne sai Ciyaman din da Kansilolin su ka fice su ka bar su, wasu har da zage zage da jifan su da duwatsu. Yin hakan raini ne da kuma barazana ga Majalisar, in ji Kabir.

A halin yanzun dai Majalisar ta kafa Kwamitin mutum 5, karkashin jagoranci Malik Bosso, don gudanar da bincike game da wannan rashin ladabi. Majalisar na bukatan rahoton binciken nan da mako 8, alhali Ciyaman din da Kansilolin su na dakace na tsawon lokacin.

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel