Jerin sunayen jihohi 5 mafi kazanta a Najeriya

Jerin sunayen jihohi 5 mafi kazanta a Najeriya

Ranar 5 ga watan Yuni ce rana ta tsaftace muhalli na Duniya wanda majalisar dinkin duniya ta ware.

Majalisar ta nusar da muhimmanci dake tattare da tsaftace muhalli da kuma yadda hakan ce magance barazanar yanayi irinsu ketowar hamada sakamakon sare bishiyoyi, dumamar yanayi da sauransu.

Duk da kokarin da gwamnatin Najeriya ke yi na tsaftace muhalli domin kaucewa wadannan matsala, an bayyana wasu jihohi 5 mafi kazanta a kasar.

Jerin sunayen jihohi 5 mafi kazanta a Najeriya
Jerin sunayen jihohi 5 mafi kazanta a Najeriya

1. Jihar Ekiti: Bincike da Community-led Total Sanitation (CLTS) ta gudanar ya nuna ta cewa jihar Ekiti ce jiha mafi kazanta wanda sama da rabin mutanen dake zaune a sashin na bahaya ne a filin Allah ta’alla.

2. Jihar Lagas: Ta kasance ta biyu a jihohi mafi kazanta a Najeriya saboda dumbin jama’a dake zaune a cikinta.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa Buhari ke bukatan goyon bayan mu – Kungiya

3. Jihar Benue: Duk da makeken rafin dake cikin ta, Jihar nada karancin ruwan sha mai kyau inda jama’ar ta ke zubda bola a madatsar wucewar ruwa.

4. Jihar Oyo: Ta kasance jiha ta uku da tafi yawan jama’a a Najeriya, kamar jihar Legas itama yawan jama’a ne sanadiyan gurbacewar muhallin ta.

5. Jihar Abia: Sakamakon cewa mafi yawancin kayan da ake kerawa a Najeriya na daga jihar Abia ne a garin Aba da kuma yashewar ruwa dake gurbata muhalli yasa jihar ta shiga cikin jihohi mafi kazanta a kasar.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

KU LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel