Cacar baki akan ruwan ledan naira 20 yayi sanadiyyar kisan wani angon gobe a Bauchi

Cacar baki akan ruwan ledan naira 20 yayi sanadiyyar kisan wani angon gobe a Bauchi

Wani matashi mai suna Shamwilu Shehu ya gamu da ajalinsa a hannun yan kato da gora dake unguwar Wunti na jihar Bauchi, bayan takaddamar data shiga tsakaninsa da wata yarinya mai siyar da ruwa.

Jaridar Aminiya ta ruwaito matashin ya siya ruwan ne a hannun yarinyar, inda ya bata Naira hamsin, ya siya na naira ashirin, yana tsammanin ta bashi canjin naira talatin, sai dai yarinyar ta ki amincewa ta amshi naira Hamsin din, inda tace kudin ya yayyage, ba mai kyau bane, kuma ba zata iya amsan kudin ba.

KU KARANTA: Yaki da ta’addanci: Sojoji sun mayar da biki akan yan Boko Haram, sun kashe mutum 42

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Shamwilu ya ki canza mata kudin, inda yace zata karbu, don kuwa shima bashi aka yi a wajen sana’ar siyar da naman da yake yi, ana cikin wannan cacar baki sai yarinyar ta zage shi.

Cacar baki akan ruwan ledan naira 20 yayi sanadiyyar kisan wani angon gobe a Bauchi
Shamwilu

Shi kuwa ya zabga mata mari, daga nan ne ta kira yayanta, wanda yana daya daga cikin yan kwamitin matasan unguwar Wunti, shi kuma ya kira abokansa Uwaisu Ahmed, Adamu Abdullahi da Shamsuddin Abubakar suka lakada masa dan banzan duka.

Bilal shehu, dan uwan Shamwilu yace bayan dawowar yayansa gida, basu san abinda ke damunsa ba, amma sun tarra da shi yana ta zazzabi, har ma yana aman jini, wanda hakan yasa suka dauka ko zazzabi ne ke damunsa, bayan sun kai shi asibiti.

A can Asibitin ne Shamwilu ya rasu, kuma sai bayan rasuwarsa ne yan uwansa suka samu cikakken bayanai dake suka tabbatar abinda yayi sanadiyyar mutuwar sa, duka daya ci a hannun yan kwamitin UnguwarvWunti.

Da jin labarin mutuwar matashin, sai yan uwan yarinyar da ta samu matsala da Shamwilu suka garzaya da ita zuwa Asibiti, da nufin ai ita ma Shamwilu ya ji mata ciwo, kamar yadda yan uwan shamwilu suka fada.

Amma yan Uwanta sun tabbatar da cewa bayan marin da Shamwilu yayi mata yayin da suka rikici, ta fadi, kuma ciwon aljanunta sun tashi, sakamakon haka ta ji rauni a jikinta.

Bayan rasuwar Shamwilu, wanda har ya kai Sadakin aurensa, yan uwanshi sun gano ashe har ya kai mutanen da suka yi masa duka kotu Musulunci dake unguwar Kobu, karkashin alkali Aminu Ilelah kafin rasuwarsa, bayan ganin takardar karar daya shigar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Jaridar Legit.ng Hausa ta kawo maku hanya mafi sauki da zaku iya karanta labaranta

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel