Karanta wasika mai sosa rai sojoji suka aika ga shugaba Buhari da Buratai

Karanta wasika mai sosa rai sojoji suka aika ga shugaba Buhari da Buratai

Sojojin Najeriya dake aikin samar da zaman lafiya a Maiduguri karkashin kirarin "Ofireshon Lafiya Dole" sun aike da wata wasika ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma babban hafsan sojin kasa na kasa, Laftanal janar Tukur Yusuf Buratai a matsayin martani ga wasikar da ya aike ma su.

Buratai ya aika wasika ga sojojin yana mai ba su karfin gwiwa tare da kiran su da kada su gajiya har sai zaman lafiya ya dawo yankin arewa maso gabas. Sannan ya dauki alkawarin ganin an biya sojojin alawus din su na watanni biyu.

Karanta wasika mai sosa rai sojoji suka aika ga shugaba Buhari da Buratai
Karanta wasika mai sosa rai sojoji suka aika ga shugaba Buhari da Buratai

A wata wasika da sojojin suka aika ranar litinin kamar yadda jami'an soji; Pte Samson Okwudili da Sajan Aliyu Bala, suka sanyawa hannu sun tabbatarwa da shugaba Buhari da Buratai cewar ba zasu gajiya ba har sai sun tabbatar da zaman lafiya ya dawo yankin na arewa maso gabas, tare da bayyana cewar wasikar ta shugaban nasu ta matukar basu karfin gwiwa.

KU KARANTA: Auren Dole: Yarinyar da aka sace ta samu kubuta daga fadar Sarki

Sojojin sun nuna matukar jin dadinsu da kulawar da Buratai tare da gwamnatin tarayya ke basu, tare da bayyana cewar hakan na kara ma su karsashin yakar ta'addanci tare da kara cusa kishin kasa cikin zukatan su. Sun bayar da tabbacin ba zasu ba wa shugaban na su da kasa kunya ba a yakin da suke yi da kungiyar Boko Haram duk kuwa da cewar su ma mayakan kungiyar ba a zaune suke ba ta bangaren ganin sun nunawa duniya cewar har yanzu suna da karfin su.

Daga karshe sojojin sun mika godiyar su ga gwamnatin shugaba Buhari da kuma jagorancin Ministan tsaro, Mannir Dan Ali, bisa hadin kai da goyon baya da suke ba wa hukumar sojin.

Labari da dumin sa: Jaridar Legit.ng Hausa ta kawo maku hanya mafi sauki da zaku iya karanta labaranta

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel