Sirraka 7 na ganyen Alayyahu a jikin dan Adam

Sirraka 7 na ganyen Alayyahu a jikin dan Adam

Alayyahu wani koren ganye da ake amfani da shi a sassa daban-daban a fadin duniya wanda kowa na iya saye saboda rashin tsada ta fuskar kudi. Ya kuma samo asali ne daga dangin abinci da turawa ke ce Amarantaceae.

Wannan ganye ya kunshi sunadaran gina jiki da inganta lafiyar dan Adam da suka hadar da; niacin, zinc, protein, folate, calcium, iron, beta-carotene, luthene, xanthene, chlorophynyll, magnesium, phosphorus, potassium, copper da kuma manganese.

Masana kiwon lafiya suna shawartar al'umma da su yi riko da wannan ganye a mu'amalolinsu na yau da kullum da abinci, sakamakon wannan sunadarai da ya kunsa domin inganta lafiyar jiki da suka hadar da;

1. Inganta karfin gani sakamakon sunadaran beta-carotene, luthene da xanthene. Wannan sunadarai su na kuma warkar da cututtukan idanu na dan Adam.

Sirraka 7 na ganyen Alayyahu a jikin dan Adam
Sirraka 7 na ganyen Alayyahu a jikin dan Adam

2. Sunadaran folate, potassium da antioxidants dake kunshe a cikin alayyahu su kan kawar da cutar kwalkwalwa da a turance ake kiranta Alzheimer's.

3. Kawar da cutar hawan jini tare da bude tashoshin da magudanan jini. Su na kuma kawar da cututtukan zuciya.

KARANTA KUMA: Lafiya Jari: Amfani 6 na ganyen Lalo ga lafiyar dan Adam

4. Ganyen Alayyahu ya kunshi sunadaran vitamin K, manganese, zinc, copper, phosphorus da kuma magnesium da suke inganta karfin kashi na jikin dan Adam.

5. Kariya da kuma warkar da cutar gyambon ciki wato Ulcer.

6. Sunadaran folate, tocopherol da kuma chlorophyllin su na warkar tare da bayar da kariya ga cutar daji musamman ta mama na mata da hanji na cikin dan Adam.

7. Kare fatar dan Adam daga cututtuka.

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel