Hanyoyin inganta Lafiya 7 da Namijin Goro ke yi a Jikin dan Adam

Hanyoyin inganta Lafiya 7 da Namijin Goro ke yi a Jikin dan Adam

Namijin goro ya samo asali ne a wasu yankunan nahiyyar Afirka, kuma ya kan zubo 'ya'ya masu launin makuba. 'Ya'yan su kan yi girma kimanin inci 3 zuwa 5, kuma ana cin sa ne da zarar an bare bawon bayan sa.

Wannan suna na namijn goro ya samo asali ne sakamakon dandanon daci dake gare shi. Kabilar yarbawa su kan kira shi Orogbo, yayin da Inyamurai ke kiran shi da sunan Akiilu, sai kuma sunan shi a turance Bitter Kola.

Legit.ng ta fahimci cewa, shekaru aru-aru ana amfani da namijin goro a al'adu daban-daban da kuma fannin kiwon lafiya wato yana magance wasu nau'ukan cututtuka a jikin dan Adam.

Hanyoyin inganta Lafiya 7 da Namijin Goro ke yi a Jikin dan Adam
Hanyoyin inganta Lafiya 7 da Namijin Goro ke yi a Jikin dan Adam

Shi dai Namijin goro yana da arzikin sunadaran dumeric flavonoids da lipase inhibitor wanda masana kiwon lafiya suka tafi akan cewa sunadaran su na magance cututtuka da dama.

Ga sirrika 7 na kiwon lafiya da namijin goro ya kunsa.

1. Namijin goro ya kunshi sunadaran quinones da kolaviron wanda ke warkar da zazzabin cizon sauro a wani bincike da aka gudanar a shekarar 2010, kuma aka buga a mujallar Medicinal Plants Research a Jamhuriyyar Kasar Congo.

2. Bincike ya nuna cewa, sunadaran antioxidants dake cikin namijin goro suna inganta lafiyar Hunhu.

KARANTA KUMA: Lafiya Jari: Sirrika 7 dake tattare a jikin tsamiya

3. A wani bincike da aka gudanar aka gudanar a birnin New York na kasar Amurka ya bayyana cewa, yana kawarda cutar idon nan ta Glaucoma.

4. Amfani da namijin goro yana hana teba da rage nauyin jiki, domin kuwa yana sanya shan ruwa matuka.

5. Sunadarin saponin da antibiotic dake kunshe a namijin goro sukan taimaka wajen karfi da tasirin kwayoyin cutar kanjamau.

KARANTA KUMA: Lafiya Jari: Amfani 6 na ganyen Lalo ga lafiyar dan Adam

6. Namijin goro yana kara karfin mazakuta ga maza ma'aurata.

7. A wani bincike da aka gudanar a jami'ar Obafemi Awolowo ta Najeriya a shekarar 2008 ya bayyana cewa, namijin goro ya kan cire kasalar jiki tare da kawar da ciwon gabbai.

Wani amfani da shukar namijin goro ke yi shine, tana korar micizai daga wuri. Idan ba a manta ba kuma, Farfesa Maurice Iwu na Najeriya ya bayyana cewa, za a iya magance cutar Ebola ta hanyar amfani da namijin goro.

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel