Kungiyar Ohanaeze ta yi Allah wadai da nadin sakataren gwamnatin tarayya

Kungiyar Ohanaeze ta yi Allah wadai da nadin sakataren gwamnatin tarayya

Kungiyar nan mai kare muradun yan kabilar Igbo wato Ohanaeze ta yi Allah wadai da nadin Mustapha Boss da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a matsayin sabon babban sakataren gwamnatin tarayya.

A cewar kungiyar sake nada sakataren gwamnatin tarayya da gwamnatin Buhari tayi daga yankin da ba nasu ba ya sake tabbatar da cewa an mayar dasu saniyar ware.

A baya NAIJ.com ta ruwaito cewa Boss Mustapha, sabon sakataren gwamnatin tarayya ya kama aiki cikin kasa da sa’o’I 24 bayan an gurbin Babachir Lawal da shi.

KU KARANTA KUMA: Za’a yi janai’izar matar sanata Goje, Hajiya Fatima Yelwa a gobe Juma’a

An kori Lawal gabaki daya a ranar Litinin, 30 ga watan Oktoba, yan watanni bayan majalisar dattawa ta zarge shi da karkatar da wadansu kudade da ya kamata ayi ma yan arewa maso gabas da Boko Haram suka addaba aiki.

Bayan nada shi a matsayin sabon sakataren tarayya, Mustapha ya bi ayarin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) don halartan taron masu ruwa da tsaki da shugaban kasa Buhari ya jagoranta a fadar shugaban kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sake zaben Osun: Omisore ya hadu da Oshiomhole, gwamnonin APC, ya amince da yiwa jam’iyya mai mulki aiki

NAIJ.com
Mailfire view pixel