Dan wasa Neymar Jr. ya ji dama bai koma Kungiyar PSG ba

Dan wasa Neymar Jr. ya ji dama bai koma Kungiyar PSG ba

- Dan wasa Neymar yana da-na-sanin barin Kungiyar Barcelona

- Rahotanni daga Kasar Sifen sun ce Dan kwallon ya gamu da cikas

- Neymar Jr. ya samu matsala da Dan wasan PSG Edison Cavani

Rahotanni daga Jaridun Sifen sun ce Dan wasan Duniya mafi tsada watau Neymar yayi babban da-na-sani a rayuwar sa na barin Barcelona.

Dan wasa Neymar Jr. ya ji dama bai koma Kungiyar PSG ba
Neymar Jr. tare da Veratti a Kungiyar PSG

Kwanakin baya Neymar Jr. ya bar Kungiyar Barcelona zuwa PSG kan makukun kudin da Duniya ba ta taba gani ba. Dan wasan dai ya zura kwallaye har 10 daga komawar sa Kungiyar amma da alamu abubuwa ba su tafiya daidai yanzu haka.

KU KARANTA: Ta bar gidan su domin ta hadu da Adam Zango

Dan kwallon gaban na Brazil ya gamu da cikas inda rikici ya barke tsakanin sa da Dan wasan gaban Kungiyar Edison Cavani kwanakin baya. Haka kuma Dan wasan yana samu matsala da Kocin Kungiyar Unai Emery game da yanayin horaswar sa.

Majiyar ta mu tace Neymar Jr. ya ji dama bai bar Kungiyar sa ta Barcelona zuwa PSG ba a karshen kakar da ta wuce. Ko a wasan da ya buga karshe a Gasar Ligue 1, Dan wasan ya tashi ne da jan kati.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel